Home Labaru Alhini: Mutuwar Isma’ila Isa Funtua Ta Bar Babban Giɓi – Shugaba Buhari

Alhini: Mutuwar Isma’ila Isa Funtua Ta Bar Babban Giɓi – Shugaba Buhari

193
0
Abin Da Igbo Za Su Yi Don Samun Shugabancin Nijeriya - Isa Funtua
Abin Da Igbo Za Su Yi Don Samun Shugabancin Nijeriya - Isa Funtua

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaɗuwarsa kan rasuwar amininsa Malam Isma’ila Isa Funtua wanda ya rasu a jiya Litinin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwa da kuma al’ummar Jihar Katsina da ma sauran makusantan marigayin bisa rasuwarsa.

Shugaba Buhari cikin wata sanarwa mai ba shi shawara kan kafafen yaɗa labarai  Garba Shehu ya fitar ya bayyana marigayin a matsayin mutum na kowa da ake matuƙar girmamawa.

Malam Isma’ila Isa Funtua yana cikin manyan wadanda ake ganin suna da tasiri a gwamnatin Buhari, kuma tsakanin wata uku dai yanzu shugaban ya rasa manyan aminansa guda biyu bayan rasuwar Abba Kyari shugaban ma’aikatan fadarsa da ya rasu watan Afrilu.

Marigayin ya taba rike mukamin minista sannan ya taba jagorantar kungiyar masu buga jarida ta NPAN na tsawon shekara takwas.

Shine kuma ya assasa kamfanin Bulet International, babban kamfanin ƙere-ƙere da ya gina muhimman wurare a birnin Abuja