Home Labaru Kiwon Lafiya Saudiyya: Sarki Salman Na Kwance A Gadon Asibiti

Saudiyya: Sarki Salman Na Kwance A Gadon Asibiti

269
0

Rahotannin da su ke fitowa daga gidajen jaridun kasar Saudiyya sun tabbatar da cewa an kwantar da sarkin mai shekaru 84 a asibiti.

Kamfanin dillacin labarai na kasar Saudiyya,  ya ce an dai kwantar da Salman Abdul’aziz ne a wani asibiti dake babban birnin Riyadh.

Bayan rahotannin cewa Sarki Salman ‘Dan Abdul’aziz ya na fama da kumburi a mafitsarar sa, babu wani labari da aka samu game da halin da yake ciki.

Yanzu haka ana yi wa Sarkin na Saudiyya, kuma mai kula da masallatan musulunci masu tsarki dake biranen Makkah da Madina gwaje-gwaje a asibiti.

Dattijon Sarkin ya yi shekaru biyar ya na mulki, amma ana ganin babban ‘dansa kuma yarima mai jiran gado Mohammed ‘dan Salman ya ke jan ragamar kasar.

Sakamakon rashin lafiyar da ta kama Sarkin, Firayim Ministan kasar Iraki, Mustafa al-Kadhimi, ya dakatar da ziyarar da ya yi niyyar kai wa zuwa kasar Saudi.

Leave a Reply