Home Labaru Alhazan Nijeriya 2139 Sun Isa Kasa Mai Tsarki – NAHCON

Alhazan Nijeriya 2139 Sun Isa Kasa Mai Tsarki – NAHCON

484
0
Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON
Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON

Mukaddashin sakataren kungiyar da ke kula da alhazan Najeriya a kasa mai tsarki Ahmad Maigari ya tabbatar da cewa mahajjatan Najeriya 2139 sun isa kasar Saudiyya domin aikin Hajjin 2019.

Ahmad Maigari, Sakataren Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON
Ahmad Maigari, Sakataren Kungiyar Kula Alhazan Najeriya Ta Kasa, NAHCON

Maigari, ya bayyana hakan ne ga magana manema labarai, inda ya ce  mahajjatan sun isa kasar a jirage uku daga jihohin Lagas, Katsina da kuma Kano, inda ya kara da cewa an ba mahajjatan masauki a Markassiya, kusa da masallacin manzan Allah S.A.W dake  Madinah,

Maigari, ya ce a kokarin ganin an hana lamarin damfara, hukumar kula da jindadin alhazai na jihohi, sun wayar da kan Musulmai akan su ziyarci wuraren ‘yan sauyin masu rijista, maimakon sauyin  kudi a kasuwar bayan fage.

Leave a Reply