Hukumar tsaro ta Civil Defence za ta rarraba karin jami’an ta dubu 15 zuwa gonaki domin samar da tsaro ga monama a wannan shakarar ta 2019.
Babban kwamandan rundunar, Abdullahi Muhammadu, ya bayyana haka a wata zantawa da ya yi da kanfanin dillancin labarai na Najeriya a Maiduguri na jihar Borno.
Rundunar ta rarraba kusan jami’ai dubu 2500 domin su magance matsalar fada a tsakanin makiyaya da manoma a farkon wannan shekarar.
Karanta Labaru Masu Alaka: Ya Kamata Ayi Amfani Da Mafarauta – Sarki Sanusi
Muhammdu, ya bayyana cewa jami’ai dari 750 za su samu horo na makonni biyar kafin a rarraba su a wurare guda takwas da ke fama matsalolin yan ta’adda a jihar Katsina.
Ya bayyana cewa jami’an za su samu horo akan yadda ake bada taimakon gaggawa da dubarun yaki da kuma yadda ake gano bam da yadda ake cire shi da sauran matakan samar da tsaro.
Ya bayyana rashin jin dadin shi game da rahotanni dake yawo cewa yan ta’adda sun hallaka manoma da yawa a cikin gonakin su, wasu kuma da yawa an tarwatsa su sakamakon hare-hare.