Home Labaru Albashin Hadiman Buhari, Osinbajo Ya Tsaya

Albashin Hadiman Buhari, Osinbajo Ya Tsaya

396
0

An dakatar da dukkan albashi da alawus-alawus na hadiman Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Wadanda aka dakatar da albashin na su kuwa sun hada da duk wadanda wa’adin aikin su ya kare daga ranar 28 ga watan Mayu na shekara ta 2019, kuma ba a sabunta masu takardar ci-gaba da aiki ba.

Wata majiya ta ce, ma’aikatan da lamarin ya shafa su na fuskantar matsala, domin babu wanda aka biya shi albashin watan Yuni kuma an dakatar da duk alawus-alaus da su ke karba.

Sama da wata daya kenan tun bayan sake rantsar da shugaba Buhari karo na biyu, amma har yau bai sabunta nadin ma’aikatan ba kuma bai kore su ya nada sabbi ba.

Wannan katankatana ta rashin sallamar ma’aikatan dai ta haifar da surutai a Nijeriya, inda lauyoyi ke cewa haramun ne a tsarin dokar kasa a bar ma’aikatan na ci-gaba da aiki bayan wa’adin aikin su ya cika.

Leave a Reply