Rahotanni na cewa, ana zargin tsohon ministan masana’antu da zuba hannun jari Okechukwu Enelamah, da tsohon ministan kasafi Udoma Udo Udoma da laifin taka rawa a wata cuwa-cuwa da ta janyo ‘yan Nijeriya 65,000 su ka yi asarar dala biliyan biyu a bankuna.

An dai kaddamar da bincike a kan ministocin biyu ne, biyo bayan korafin da aka kai wa Atoni Janar na Nijeriya Abubakar Malami a ranar 3 ga watan Afrilu na shekara ta 2019.
Takardar karar mai taken ‘Almundahana’, ta koka a kan babakeren dala bilyan biyu da rashin adalci wajen azurta wasu ‘yan kalilan ta hanyar talauta ‘yan Nijeriya 65,000 masu hannun jari a bankuna.
Ana dai zargin ministocin da amfani da kujerun su wajen danne wasu ‘yan Najeriya 65,000 da su ka zabu jari saboda jin dadin wasu masu hannu da shuni.
You must log in to post a comment.