Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 A Katsina

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 15 A Katsina

485
0

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane goma sha biyar a wani hari da su ka kai a kauyuka hudu da ke kananan hukumomin Kankara da Danmusa a jihar Katsina.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun fara kai hari a Unguwar Nagwande da misalin 4:30 na yamma su ka kashe mutane hudu, daga nan su ka shiga Unguwar Rabo su ka kashe mutane tara, sannan sun sake kai hari Gidan Daji inda su ka kashe mutane biyu.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun shiga kauyen Maidabino a karamar hukumar Danmusa, inda su ka bude wuta a cikin kasuwar garin yayin da mutane ke hada-hadar kasuwancin su.

Mutane da da dama sun mutu, yayin da wasu su ka samu munaman raunuka, daga bisani mutanen kauyukan su ka kwashe gawarwakin, sannan su ka dunguma zuwa fadar Sarkin Katsina domin kai kukan su a kan lamarin.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Kastina SP Gambo Isah, ya ce mutane 11 ne kawai aka kashe a karamar hukumar Kankara, sannan an sake kashe mutane biyu a kauyen Maidabino.

Leave a Reply