Home Labaru Bayan Mutuwar Maryam: IBB Ya Ce Ya Na So Ya Sake Yin...

Bayan Mutuwar Maryam: IBB Ya Ce Ya Na So Ya Sake Yin Wani Aure

580
0
Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida
Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya shafe tsawon shekaru 40 ya na zaune tare da matar sa marigayiya Maryam kafin mutuwar ta a watan Disamba na shekara ta 2009.

Marigayiya Maryam dai ta yi suna a Nijeriya ne, saboda irin tasirin da ta ke da shi a kan mijin ta da kuma soyayyar da ke tsakanin su.

Yayin wata tattaunawa da manema labarai, Janar Babangida ya ce har yanzu bai daina jin radadin mutuwar Maryam ba, duk kuwa da tsawon lokacin da ya shude tun bayan komawar ta ga mahalicci.

Sai dai, duk da irin kewar ta da jin radadin rayuwa ba da marigayiyar ba, Babangida ya ce ya na son zai sake yin wani aure.

Janar Babangida ya kara da cewa, da gaske ya ke yi cewa ya na son sake yin aure saboda tsufa ya ke kara yi, don haka akwai lokacin da bukatar abokiyar zama ba zai yi ma shi wata rana ko amfani ba.