Hukumar bada agajin gaugawa ta kasa NEMA, ta ce ta na iyakar kokarin ganin ta kubutar da jami’an ta da aka yi garkuwa da su.
Babban jami’in kula da sashen dakile fargaba da aukuwar ibtila’i Vincent Owan ya bayyana haka, yayin da ya ke zantawa da manema labarai a birnin Port Harcourt na jihar Rivers.
Ya ce an yi garkuwa da mutanen ne a lokacin da su ke aikin kai kayayyakin tallafi ga wasu mabukata ranar Talatar da ta gabata a Ahoada da ke jihar Rivers.
Jami’in ya cigaba da cewa, yanzu haka hukumar ta na gudanar da aikin rabon kayayyakin tallafi a jihohi 17 ciki kuwa har da jihar Rivers.
You must log in to post a comment.