Home Labaru Akwai Raɗe-Raɗin Korar Ministoci Bayan Taron Bin Diddigin Ayyukan Su

Akwai Raɗe-Raɗin Korar Ministoci Bayan Taron Bin Diddigin Ayyukan Su

11
0

Akwai yiwuwar Shugaba Muhammadu Buhari ya sake korar wasu ministoci bayan kammala taron bin diddigin ayyukan su.

Taron na kwanaki biyu a karkashin jagorancin shugaba Buhari, an shirya shi ne domin bitar ayyukan ministocin da nasarorin da su ka samu ko akasin haka.

Shugaba Buhari, ya ce zai zauna har zuwa karshen taron domin sauraren bayanan kowane minista da nasarori da yanayin ayyukan su cikin shekaru biyu da su ka gabata.

Yayin gabatar da jawabin sa, Buhari ya gargadi ministoci da manyan sakatarorin ma’aikatu su maida hankali wajen ayyukan da su ka rayata a wuyan su domin ci-gaban gwmanatin sa.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Satumba ne ya kori ministocin sa biyu, sakamakon rashin taka rawar gani a ayyukan su, kuma sun kasance ministocin farko da ya kora tun hawan sa mulki a shekara ta 2015.