Home Labaru Gwamna El-Rufai Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Shekara Ta 2022

Gwamna El-Rufai Ya Gabatar Da Kasafin Kudi Na Shekara Ta 2022

10
0

Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna, ya gabatar da kasafin kudi na shekara ta 2022, na naira biliyan 233 ga majalisar dokoki ta jihar Kaduna.

Kasafin kudin, ya na dauke da bayanin kashe Naira biliyan 146 a fannin ayyuka da jari da na Kashewa akai-akai, wanda ya kai Naira biliyan 87 da Miliyan 600.

El-Rufa’i ya yi nuni da cewa, rabe-raben da aka yi a cikin alkaluman kasafin, sun yi nuni da kimar siyasa da ka’idojin shugabanci, wanda a ko da yaushe su ke jagorantar kasafin kudi shida na baya da gwamnatin sa ta gabatar.

Ya ce alkaluman shekara ta 2022, sun yi kasa da kasafin kudi na shekara ta 2021 na Naira Biliyan 237 da Miliyan 52, wanda ke da Naira Biliyan 157 da Miliyan 56 na ayyuka da jari, da kuma Naira Biliyan 79 da Miliyan 96 da aka tsara domin kashewa akai-akai.

A wata sanarwa da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar a shafin ta na Facebook, El-Rufa’i ya ce abubuwan da aka sa gaba na kasafin shekara ta 2022, sun hada da Ilimi da Kiwon Lafiya da Kayayyakin more rayuwa kamar dai na kasafin baya.