Home Labaru Aisha Buhari Ta Karbi Bakuncin Takwarorinta A Abuja

Aisha Buhari Ta Karbi Bakuncin Takwarorinta A Abuja

200
0

An buɗe taron ƙoli na ƙungiyar Matan Shugabannin ƙasashen Afirka a nan babban Birnin Tarayya Abuja.

Uwargidan shugaban Najeriya kuma mai masaukin baƙi, Aisha Buhari ce za ta aza harsashin gina Sakatariyar Dindindin ta ƙungiyar.

Wannan Taron dai ya ƙunshi liyafar tara gundunmuwa domin bunkasa sakatariyar kungiyar.

Matan shugabannin Afrika masu yawa ne da manyan ‘ƴan kasuwa da masu masana’antu ke halartar taron.

Tuni matan shugabannin Afrika da suka hada da na Burundi da Congo Brazzaville da Sao Tome da Saliyo ke halartar taron.

Suran sun hada da matan shugabannin Ghana da Cote d’Ivoire da Nijar da Liberia.

Wata Sanarwar da ofishin yada labarai na uwargidan shugaban Najeriya ya fitar ta ce an kafa ƙungiyar tabbatar da zaman lafiya ta shugabannin matan Afrika ne a shekarar 1997 domin goyon baya ga Tarayyar Afrika da ƙungiyoyin ƙasashen yankin da kuma gwamnatocin yankin.

Tuni dai Matan shugabannin kasashen Afirka, sun kawo karshen taronsu inda suka tattauna dangane

Leave a Reply