Home Labaru Jam’iyar APC Zata Gudanar Da Taron Ta Na Kasa A Watan Fabrairun...

Jam’iyar APC Zata Gudanar Da Taron Ta Na Kasa A Watan Fabrairun Badi

60
0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a sanya watan Fabrairun shekarar 2022 a matsayin lokacin gudanar da babban taro tare da zaben shugabannin jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC uma Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu ne ya sanar da hakan, jim kadan da kammala ganawar sirri da Shugaba Buhari a Fadar Shugaban Kasa da ke nan Abuja.

Taron dai ya samu halartar Shugaban riko na jam’iyyar, kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da kuma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar.

Bagudu ya ce an zabi watan na Fabrairu ne domin baiwa Jihohi hudu da ba su gudanar da zaben ba su yi hakan, tareda kammala shagulgulan watan Disamba mai zuwa.

A nasa tsokacin, Gwamna Mai Mala ya ce watan kawai aka tsayar, amma ba sa ranar gudanar da zaben ba, kuma tuni sun aike da bukatar hakan ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) sannan sun tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.