Home Labaru Rahoton ENDSARS: Dan Majalisar PDP Ya Nemi Buhari Ya Tsige Lai Mohammed

Rahoton ENDSARS: Dan Majalisar PDP Ya Nemi Buhari Ya Tsige Lai Mohammed

35
0

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, ya bukaci ministan yada labarai da al’adu Lai Mohammed ya gaggauta yin murabus ko kuma shugaba Muhammadu Buhari ya sallame shi daga aiki.

Kiran dan majalisar dai, martani ne ga sharhin da Lai Mohammed ya yi a baya game da kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zangar EndSARS a Lekki Toll Gate, kafin kwamitin binciken lamarin ya fitar da rahoton sa.

Rahoton kwamitin dai ya bayyana lamarin a matsayin kisan-gilla, sabanin matsayar Lai Mohammed na baya.

Ndudi Elumelu, ya ce ya yi mamakin dalilin da ya sa ministan Lai Mohammed da ya san gaskiya shiga kafofin watsa labarai kafin kwamitin bincike, har ya rika cewa lallai ba a kashe kowa ba a Lekki Tollgate.