Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli,
wanda ya jagoran Alhazan jihar Kaduna a matsayin Amirul
Hajjin bana, ya ce aikin hajjin bana ya na cike da matsalolin
da ya kamata mahukunta su duba domin su sauya salo.
Wannan dais hi ne karno farko da gwamnatin jihar Kaduna ta nada Mai Martaba Sarkin Zazzau a matsayin Amirul Hajji tun bayan nadin sa, ya na mai cewa abubuwan da ya gani na gazawa a aikin Hajjin bana su na da sosa rai matuka.
Yayin da ya ke yi wa al’ummar masarautar Zazzau jawabi bayan dawowar sa daga kasa mai-tsarki, Basaraken ya ce shi kan sa sai da ya raba tawagar shi gida uku.
Idan dai ba a manta ba, tun kafin tashi zuwa kasar Saudiya an samu takun-saka tsakanin Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar Kaduna Malam Yusuf Yakub Arrigasiyyu da Hukumar Alhazai ta kasa, a kan matsalar wasu kujerun masu kudin adashe sakamakon jinkirin da aka samu wajen samun takardar
izinin zuwa Saudiyya.
Duk da nasarar da aka samu wajen jigilar Alhazai zuwa kasa mai tsarki a bana dai, an ci karo da matsalolin masaukai a Makka da Madina da kuma Mina, sannan dawo da Alhazan zuwa Nijeriya ya na shan korafe-korafe saboda rashin sauri.