Home Labaru Gwanatin Jihar Kaduna Ta Rage Wa Ma’Aikata Kwanakin Zuwa Ofishi

Gwanatin Jihar Kaduna Ta Rage Wa Ma’Aikata Kwanakin Zuwa Ofishi

111
0

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce daga ranar 1 ga watan Disamba ma’aikatan jihar za su fara aiki kwana huɗu ne a mako.

Wata sanarwa da gwamnatin jihar ta bayar ranar Litinin tace matakin zai ba ma’aikatan damar yin aikin kwana ɗaya daga gida, domin inganta aiki da ba su damar samun lokaci ga iyalan su da kuma samun lokacin noma.

Sanarwar ta ce matakin na daga cikin darussan da aka koya lokacin annobar korona da ke buƙatar samun lokacin samun annashuwa saɓanin tsohon tsarin da aka saba da shi na aiki.

Sanarwar ta kuma ce lokacin aiki zai koma daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma daga ranar Litinin zuwa Juma’a amma ranar Juma’ar za a yi aiki ne daga gida.

Sanar ta ce matakin ya shafi dukkanin ma’aikatan jihar Kaduna sai dai banda malaman makaranta da kuma ma’aikatan kiwon lafiya.

Leave a Reply