Jam’iyyar PDP ta ce, kalaman A’isha Buhari a kan shirin gwamnatin tarayya na bada tallafi sun tabbatar da maganganun da su ka dade su na yi cewa gwamnatin APC ta na goyon bayan cin hanci da rashawa.
Da ta ke maida martani a kan sukar da A’isha Buhari ta yi a kan yadda ake sarrafa naira biliyan 500 da shugaban kasa ya ware da sunan shirin SIP, PDP ta bukaci hukumomin yaki da cin hanci su dauki matakan fara bincike a kan lamarin.
A ranar Asabar da ta gabata ne, A’isha Buhari ta ce shirin SIP ya gaza tabuka komai a arewacin Nijeriya, tare da zargin mai ba shugaban kasa shawara a kan shirin bada tallafi Maryam Uwais da rashin dacewa da mukamin da aka ba ta.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan, ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana a kan zargin da mai dakin sa ta yi tare da daukar matakin da ya dace.
Ya ce matar shugaban kasa ta nuna cewa, jam’iyyar PDP ba sharri ko kage ta ke yi wa gwamnatin APC ba, ya na mai cewa dole shugaba Buhari ya dauki alhakin duk wasu kudi da aka sace a gwamnatin sa a cikin shekaru hudu da su ka gabata.
You must log in to post a comment.