Home Labaru Yabon Gwani: Matasa Sun Bukaci Buhari Ya Bar Boss Mutapha A Kan...

Yabon Gwani: Matasa Sun Bukaci Buhari Ya Bar Boss Mutapha A Kan Mukamin Sa

276
0

An bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya cigaba da aiki tare da Boss Musatafa a matsayin sakataren gwamnatin tarayya.

Hadakar kungiyar matasan Nijeriya da kungiyoyi masu zaman kansu su ka gabatar da bukatar hakan, yayin wani taro da su ka gudanar a Birnin kano.

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar dauke da sa hannun babban jami’in ta Kwamred Nuhu Lere, ta bayyana Boss Mustapha a matsayin kashin bayan gwamnatin shugaba Buhari, duba da kwarewar sa a matsayin lauya kuma masani a fannin harkokin kasuwanci da ilimin gudanar da mulki.

Kwamred Nuhu S. Lere, ya ce Boss Mustapha ya taka rawar gani, musamman ta fuskar tsarkake alaka tsakanin bangaren zartarwa da na shari’a da kuma bangaren majalisun dokoki na tarayya.