Home Labaru Adawa Da Dimokaradiyya: Masu Zanga-Zanga Sun Buƙaci Sojoji Su Yi Juyin Mulki...

Adawa Da Dimokaradiyya: Masu Zanga-Zanga Sun Buƙaci Sojoji Su Yi Juyin Mulki A Sudan

7
0
Masu adawa da yunƙurin dawo da tsarin dimokuraɗiyya a Sudan sun fito saman titunan Khartoum a ranar Asabar suna zanga-zangar neman sojoji su ƙwace ikon ƙasar

Masu adawa da yunƙurin dawo da tsarin dimokuraɗiyya a Sudan sun fito saman titunan Khartoum a ranar Asabar suna zanga-zangar neman sojoji su ƙwace ikon ƙasar.

Dubban masu zanga-zanga sun haɗa gangamin ne a fadar shugaban ƙasa, yayin da rikicin siyasar ƙasar ke ƙara zafi.

Tun hamɓarar da shugaba Omar al-Bashir a 2019 ake mulkin karɓa-karɓa tsakanin Sojoji da fararen hula a kasar.

Sai dai fargabar rikici na ƙaruwa tun lokacin da aka yi yunƙurin juyin mulkin da aka hamɓarar wanda aka zargi magoya bayan tsohon shugaba Al Bashir a watan Satumba.

Tun lokacin shugabannin soji ke naman kawo sauyi na haɗaƙa tsakanin sojoji da kuma fararen hula da suka jagoranci zanga-zangar da ta yi sanadin kawo ƙarshen mulkin Al-Bashir a sudan, wani ɓangare na fararen hula na ganin buƙatar sojoji matakin ci gaba da mulki.