Home Labaru Ambaliya: Mutum 25 Sun Mutu A Indiya

Ambaliya: Mutum 25 Sun Mutu A Indiya

6
0
Sojoji da jami'an agaji na kokarin ceton jama'ar da suka makale sakamakon ambaliyar ruwa gami da zabtarewar kasa da suka halaka kimanin mutum 25 a kasar Indiya.

Sojoji da jami’an agaji na kokarin ceton jama’ar da suka makale sakamakon ambaliyar ruwa gami da zabtarewar kasa da suka halaka kimanin mutum 25 a kasar Indiya.

Hukumomi a Indiya sun ce kimanin mutum 25 suka halaka sakamakon zaftarewar kasa da ambaliyar rowan, Lamarin da ya auku a jihar Kerala da ke kudu maso yammacin Indiya, inda rahotanni ke cewa yanzu hakan sojoji da jami’an agajin gaggawa na ci gaba da ceton mutanen da lamarin ya shafa.

Tuni ma dai aka kafa sansanonin karbar mutane da hatsarin ya rutsa da su, a cewar gwamnan yankin a yayin da yake magana da manema labarai.

Wasu hotunan da suka karade shafukan sada zumunta, na nuna irin yadda ruwan ya mamaye motocin sufuri na mutane a yankin, kana tuni Firaministan kasar ta Indiya Narendra Modi, ya nuna alhini da ta’aziya kan wadanda suka rasa rayukan su a wani sakon da ya aike ta shafin sa na Twitter, tare da da bayyana cewa hukumomi za su kawo dauki ga wadanda abin ya shafa.