Home Labaru Yi Wa Matashi Kwace: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Ce Za A Binciko...

Yi Wa Matashi Kwace: Rundunar ‘Yan Sanda Ta Ce Za A Binciko Jami’an Ta Da Aka Gani A Bidiyo

9
0
Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya bayar da uamrnin ƙaddamar da bincike kan ‘yan sandan da aka gani a bidiyo suna yi wa wani matashi ƙwace.

Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya Usman Alkali Baba, ya bayar da uamrnin ƙaddamar da bincike kan ‘yan sandan da aka gani a bidiyo suna yi wa wani matashi ƙwace.

Cikin bidiyon da ya karaɗe shafukan zumunta, ana iya jin wanda ke ɗaukar bidiyon na cewa ‘yan sandan sun tsare matafiya ne inda suka zaƙulo wani matashi ɗauke da kwamfuta suka cusa shi a motar su.

Kazalika ya yi zargin cewa ‘yan sandan sun nemi ya ba su kuɗi amma ya ce ba shi da su a matsayin sa na ɗalibi, duk da haka suka ce ya buga waya a turo masa ta banki domin su je su cire a na’urar ATM.

Mai maganar ya ce lamarin ya faru ne a garin Okene na Jihar Kogi.

Cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar ‘yan sanda na ƙasa Frank Mba ya fitar, Usman Baba ya umarci rundunar reshen Jihar Kogi ta ƙaddamar bincike nan take.

Babban sufetan ya buƙaci a kwantar da hankali, yana mai cewa za a tabbatar da adalci da zarar an kammala binciken sannan a gurfanar da ‘yan sandan da aka kama da laifi a gaban kotu.