Home Labarai Abin Da Ya Sa Buhari Ya Dakatar Da Akanta Janar Ahmed Idris

Abin Da Ya Sa Buhari Ya Dakatar Da Akanta Janar Ahmed Idris

323
0

Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar dakatar da babban Akanta na Tarayya Ahmed Idris, kwana ɗaya bayan Hukumar EFCC ta kama shi dangane da zargin sace aƙalla naira biliyan 80 ta hanyar kwangilolin bogi.

Ministar kudi Zainab Ahmed ta fitar da sanarwar dakatar da Idris, sanarwar ta ce an dakatar da Idris ba tare da za a riƙa biyan sa albashi da alawus-alawus ba.

Hukumar EFCC dai ta kama Idris ne a Kano, inda daga can aka sanya shi a jirgi zuwa Abuja.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce ana zargin salwantar maƙudan kuɗaɗe a hannun Idris kimanin naira biliyan 80, waɗanda aka riƙa waskewa da su da sunan ayyukan kwangiloli na bogi.

Wata Majiya ta ce an gano cewa, an riƙa sayen maka- makan kadarori da kuɗaɗen a Kaduna da Abuja.

A Cikin sanarwar dakatar da shi, an umarce shi da cewa kada ya kuskura ya leƙa ofishin sa, kuma kada ya yi wata mu’amala da ko da ɗaya daga cikin ma’aikatan ofishin sa, domin kada ya yi katsalandan a cikin binciken da ake yi ma sa.

Leave a Reply