Home Labaru Tinubu Ya Naɗa Ribaɗu A Matsayin Mai Ba Shi Shawara Kan Harkar...

Tinubu Ya Naɗa Ribaɗu A Matsayin Mai Ba Shi Shawara Kan Harkar Tsaro

338
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa masu ba shi
shawara a kan harkoki daban-daban ciki har da Mallam Nuhu
Ribaɗu a matsayin mai ba shi shawara ta fuskar harkokin tsaro
na musamman.

Wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na fadar shugaban kasa Abiodun Oladunjoye ya fitar, ta ce Shugaba Tinubu ya amince da naɗe-naɗen da su ka haɗar da Mista Dele Alake a matsayin mai bada shawara a kan harkar ayyuka na musamman da sadarwa da tsare-tsare.

Haka kuma, an nada Mallam Ya’u Darazo a matsayin mai bada shawara na musamman a kan harkokin siyasa da hulɗa tsakanin gwamnatoci, sannan akwai Mista Wale Edun da aka nada a matsayin mai bada shawara na musamman a kan manufofin kuɗi.

Sauran sun hada da Misis Olu Verheijen a matsayin mai bada shawara ta musamman a kan harkokin makamashi, da Mista Zachaeus Adedeji a matsayin mai bada shawara na musamman a kan harkokin kuɗin shiga, da kuma Dr. Salma Ibrahim Anas a matsayin mai bada shawara ta musamman a fannin kula da lafiya, da Mista John Ugochukwu da aka naɗa a matsayin mai bada shawara na musamman a kan harkokin masana’antu da kasuwanci da zuba jari.

Leave a Reply