Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya sake nada Sheikh
Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin shugaban Hukumar
Hisbah ta jihar karo na uku.
A baya dai Sheikh Daurawa ya taba jagorantar hukumar har sau biyu a zamanin mulkin Rabi’u Musa Kwankwaso da farkon mulkin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Sai dai a shekara ta 2018, Daurawa ya sanar da ajiye mukamin sa lokacin da aka samu sabani tsakanin Kwankwaso da Ganduje.
A ranar Litinin din nan ne, malamin ya wallafa wani bidiyo da ya nuna ya na karbar takardar sake nada shi shugabancin hukumar karo na uku, daga Sakataren Gwamnatin Jihar Dakta Baffa Abdullahi Bichi.














































