Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi dirar mikiya a garin Ibbi na jihar Taraba, bayan kashe jami’ansu uku da wani farin hula daya, da sojoji suka yi a titin da ya ratsa garin zuwa Wukari.

Jami’an ‘yan sandan sun tafi garin ne domin farautar wani da ake zargi da laifin garkuwa da mutane mai suna Alhaji Hamisu Wadumi da ya tsere a dai-dai wurin da aka kashe ‘yan sandan uku da faran hula daya.
Mataimakin kwamishinan ‘Yan sanda Abba Kyari, ne ya jagoranci tawagar ‘yan sandan, inda wadanda aka kama suna ofishin ‘yan sanda da ke Wukari, yayin da wasu kuma aka tafi da su Jalingo.
Karanta Wannan: Gwamnonin APC Sun Dora Alhaki Rikirkita Al’amurran Jam’iyyar A Kan Adams Oshiomole
Motoccin sojoji da na ‘yan sanda fiye da 15 ne suka isa Ibbi kuma suna ci gaba da kama mutane a lokacin da muke kawo muka wannan rahoto.
Jami’an ‘yan sandan sun kwato motocci da yawa da aka ce mallakar wanda ake zargi da garkuwa da mutanen ne a gidansa da kuma wasu wurare.
Sai dai mazauna garin na Ibbi dake kusa da Rafin Benue sun yi hijira daga gidajensu domin tsoron abinda zai kai ya kawo.
You must log in to post a comment.