Home Labaru EFCC Ta Binciki Yari Kan Biliyan 251 – Shinkafi

EFCC Ta Binciki Yari Kan Biliyan 251 – Shinkafi

811
0
Abdulaziz Yari, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara
Abdulaziz Yari, Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara na jam’iyyar APGA Sani Abdullahi Shinkafi, ya bukaci shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu ya fara binciken tsohuwar gwamnatin Abdulaziz Yari.

A cikin takardar korafin da ya aike wa hukumar EFCC, Shinkafi ya zargi Abdul-Aziz Yari da almubazzarantar da naira biliyan 251 mallakin jihar Zamfara.

Karanta Labaru Masu Kama: Ban Bar Wa Jihar Zamfara Bashin Ko Sisin Kwabo Ba – Yari

Sani Abdullahi Shinkafi, Dan Takarar Kujerar Gwamnan Jihar Zamfara Na Jam’iyyar APGA
Sani Abdullahi Shinkafi, Dan Takarar Kujerar Gwamnan Jihar Zamfara Na Jam’iyyar APGA

Da ya ke bada bahasin yadda gwamnatin Yari ta tafka almundahana, Shinkafi ya ce Yari ya bar bashin Naira biliyan 151 da miliyan 190 da dubu 477 da 572 na ayyukan da ba a karasa ba.

Ya ce tsohon gwamnan ya yanki Naira biliyan 1 da miliyan 431 da dubu 645 da 303 a matsayin kudaden gidaje daga albashin ma’aikatan jihar Zamfara daga shekara ta 2016 zuwa 2019.

A karshe ya ce gwamnatin Yari ta bar bashi a ma’aikatar ilimi da kudaden jarrabawa da na wasu makarantu da ke wajen jihar da yawan su ya kai Naira biliyan 2 da miliyan 812 da dubu 172 da 155.