Home Labarai 2023: Zulum Muke So Ya Zama Mataimakin Tinubu, Masu Ruwa Da Tsaki...

2023: Zulum Muke So Ya Zama Mataimakin Tinubu, Masu Ruwa Da Tsaki ‘A APC

60
0

Jagoran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a yankin Arewa Abdullahi Aliyu Katsina, ya ce kuri’ar jin ra’ayin al’umma da kungiyar ta yi ya nuna cewa, zaben gwamnan jihar Borno Babagana Zulum a matsayin mataimakin Tinubu ne kadai zai tabbatar wa APC samun nasara cikin sauki.

Yayin taron manema labarai da aka yi Minna na jihar Neja, Abdullahi Aliyu ya ce duk da cewa mutanen Borno ba su son ya tafi saboda ayyukan alherin da ya ke yi a jihar, amma yi wa kasa hidima zai fi dacewa.

Ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne cin zaben shekara ta 2023, amma ya zama dole a tsaida mutumin da ake mutuntawa kuma an yarda da shi domin ya kawo kuri’un arewa, kuma Babagana Zulum ne kadai ke da wadannan halaye.

Abdullahi Aliyu, ya ce a halin yanzu ana bukatar dukkan ‘yan jam’iyya su jajirce su yi aiki domin ganin jam’iyyar APC ta yi nasara a zaben shekara ta 2023.