Home Labarai Ba Zan Shiga Wata Jam’iyya Ba Kafin Zaben 2023 – Moghalu

Ba Zan Shiga Wata Jam’iyya Ba Kafin Zaben 2023 – Moghalu

165
0

Daya daga cikin wadanda su ka nemi tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ADC Farfesa Kingsley Moghalu, ya ce ba zai shiga wata jam’iyya ba kafin zaben na shekara ta 2023.

Moghalu dai ya fice daga jam’iyyar ADC ne bayan ya fadi a zaben fidda gwani, inda Dumebi Kachikwu ya yi nasara a zaben da aka yi a birnin Abeokuta na jihar Ogun.

A wata sanarwa da ya fitar, Kingsley Moghalu ya ce bayan shawarar da ya yi da iyalai da abokan sa cikin natsuwa, ya zartar hukuncin cewa ba zai tsaya takarar ba kamar yadda wasu jam’iyyu ke gayyatar sa ya yi ma su takara a karkashin tutar su.

Moghalu ya ce zai cigaba da bada goyon baya da gudunmuwa ga zaben shekara mai zuwa domin amfanin kasar sa Nijeriya, sannan ya shaida ma wadanda su ka samu tikitin takara a karkashin jam’iyyar cewa ya na tare da su zai kuma yi masu fatan nasara.

Leave a Reply