Home Labarai 2023: Mata 380 Su Ka Fito Takara A Zaɓen Majalisar Dattawa Da...

2023: Mata 380 Su Ka Fito Takara A Zaɓen Majalisar Dattawa Da Ta Tarayya – INEC

30
0

Hukumar Zaɓe mai zaman kan ta ta Ƙasa INEC, ta ce an samu mace ɗaya tilo ta fito takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekara ta 2023.

Wannan, ya na ƙunshe ne a cikin jerin sunayen da hukumar ta fitar mai ɗauke sa hannun Kakakin Yaɗa Labarun ta Festus Okoye, inda ya ce an samu mata 380 da za a fafata neman kujerun Majalisar wakilai da ta Dattawa da su.

A jerin sunayen, an lissafa mata 92 masu neman kujerar Majalisar Dattawa, sai kuma wasu 288 da za a fafata neman kujerar Majalisar wakilai da su.

A ɓangaren maza kuwa, hukumar zaben ta buga sunayen masu neman kujerar Majalisar Dattawa dubu 1 da 8, sai kuma wasu dubu 2da 832 da za su fafata neman kujerun Majalisar wakilai.

Hukumar zabe, ta ce jam’iyyu 18 ne su ka shiga takarar zaɓen shugaban ƙasa, wanda za a fafata a ranar 25 ga watan Fabrairu na shekara ta 2023, inda aka samu masu takarar kujerar shugaban ƙasa da mataimakan su 35.