Home Labarai Wanda Za Mu Goya Wa Baya A Zaben 2023 – Manyan Arewa

Wanda Za Mu Goya Wa Baya A Zaben 2023 – Manyan Arewa

36
0

Jagororin Arewacin Nijeriya, sun ce dan takarar da zai iya magance matsalar tsaro da sauran kalubalen da ke addabar yankin su kawai za su goyi baya a zaben shugaban kasa na shekara ta 2023.

Shguabanin daga jihohi Arewa 19 da Birnin Tarayya Abuja, sun bayyana matsayin su ne a wani taron kwana biyu da kungiyar Sabuwar Ajandar Arewa ANA ta shiyra a Abuja.

Sun ce matsalar tsaro da rabuwar kai da zama koma-baya da sauran matsaloli sun hana yankin Arewacin Nijeriya samun ci-gaban da ya kamata, inda su ka nuna takaici a kan abin da su ka kira gazawar shugabanin yankin wajen daukar matakan da su ka dace wajen yi wa tufkar hanci.

Babban Sakataren Kungiyar Kare Muradun Arewa ACF, Murtala Aliyu, ya ce wajibi ne yankin ya tashi tsaye wajen tattaunawa da shugabannin siyasar Nijeriya domin tabbatar da ci-gaban yankin ba tare da bata lokaci ba.