Majalisar wakilai ta yi kira ga Hukumar Zaɓe mai zaman kan ta ta Ƙasa INEC, ta ƙara wa’adin kwanaki 60 kafin ta rufe aikin sabunta rajistar katin zaɓe.
A ranar 30 Ga wagtan Yuni ne wa’adin da hukumar zaben ta bada na daina rajistar katin zaɓen zai cika.
Neman ƙarin kwanaki 60 da majalisar ta yi dai ya biyo bayan wani ƙorafi da dan majalisa Ben Kalu ɗan ya yi a zauren a ranar larabar da ta gabata.
Majalisar wakilai ta amince da ƙorafin, inda nan take Kakakin Majalisar Femi Gbajabiamila ya umarci Kwamitin kula da Harkokin Zaɓe na Majalisar wakilai ya tuntuɓi Hukumar Zaɓe ta Ƙasa domin su tattauna yadda za a ƙara wa’adin.
Ana dai ci-gaba da samun tururuwar masu zuwa domin yin rajistar zaɓe, tun bayan kammala zaɓen fidda-gwanin jam’iyyun APC da PDP na takarar shugaban ƙasa.
You must log in to post a comment.