Home Labarai Zaben 2023: Atiku Ya Zabi Gwamnan Delta A Matsayin Mataimakin Sa

Zaben 2023: Atiku Ya Zabi Gwamnan Delta A Matsayin Mataimakin Sa

92
0

Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya zabi gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben shekara ta 2023.

Atiku Abubakar ya sanar da hakan ne, a wajen tantance ɗaukar ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasar a helkwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja.

Yayin da PDP ta fitar da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa daga kudancin Nijeriya, jam’iyyar APC kuma za ta ɗauki abokin tafiyar ɗan takarar ta ne daga yankin arewa.

An zaɓi mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP ne ta hanyar kafa wani kwamiti domin tantance mutanen da ke son mara wa Atiku Abubakar baya.