Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta yi alkawarin kama duk wasu ‘yan kasa da shekaru 18 da aka kama za su yi zabe.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar Festus Okoye ya bayyana haka, yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin Arise.
Festus Okoye, ya ce ana kokarin magance matsalar da ake samu, dangane da yadda kananan yara ke zuwa rumfunan zabe domin kada kuri’a.
Ya ce a yunkurin ganin an tsabtace tsarin zabe, hukumar ta bukaci duk jami’an ta da aka samu sun yi wa kananan rajista su bayyana a gaban wani kwamitin musamman.
Kwamishinan ya cigaba da cewa, yanzu haka su na kokarin cire snayen kananan yara daga rajistar zaben, kuma a karshe ‘yan Nijeriya za su ji dadin aikin da aka yi.