Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce Nijeriya za ta duba buƙatar taimakon makamashi, musamman man fetur da gwamnatin ƙasar Burundi ta gabatar.
A Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adeshina ya fitar, shugaba Buhari ya yi alƙawarin ne bayan ya karɓi baƙuncin ministan kuɗi da kasafi da tsare-tsare na ƙasar Burundi Audace Niyonzima a fadar sa da ke Abuja.
Sanarwar ta ce, Buhari ya tabbatar wa da Niyonzima cewa, Nijeriya za ta taimaka wa ƙasar Burundi ta hanyoyi da dama, a ƙarƙashin inuwar zumunci da ‘yan’uwantaka da ke tsakanin ƙasashen Afirka.
Shugaba Buhari, ya ce ya san yadda ƙasa ke ji musamman idan ta na fama da ƙarancin makamashi, tare da daukar alƙawarin cewa zai tura lamarin ga kamfanin NNPC domin duba buƙatar.
Buhari ya ce a yanzu batun zaɓen Nijeriya da saukar sa daga mulki ne a gaban sa, tunda dai ya yi wa’adi biyu da kundin tsarin mulki ya ba shi dama.














































