Home Labarai 2023: Dalilin Mu Na Goyon Bayan Obi Maimakon Tinubu – Ƙungiyar Afenifere

2023: Dalilin Mu Na Goyon Bayan Obi Maimakon Tinubu – Ƙungiyar Afenifere

31
0

Shugaban Ƙungiyar Kare Muradun Yarabawa Zalla ta Afenifere Ayo Adebanjo, ya ce su na goyon bayan Peter Obi na jam’iyyar Labour ne, domin idan Tinubu ya yi nasara zai cigaba da irin mulkin Shugaba Muhammadu Buhari.

A cikin wani saƙo da ta wallafa a shafin ta na Tiwita, Afenifere ta bayyana rashin goyon Bola Tinubu, wanda ɗan’uwan su ne Bayarabe kuma ɗan takarar APC, saboda a cewar su, Tinubu zai cigaba ne daga inda Buhari ya tsaya, lamarin da su ka ce ba zai yi wa ‘yan kungiyar daɗi ba.

Afenifere, ta ce, Tinubu ba ya da wani abin da zai yi na ci-gaba, illa ya cigaba da irin salon mulkin shugaba Buhari, salon mulkin da ya jefa marasa ƙarfi cikin ƙuncin rayuwa a faɗin Nijeriya.

Sun ce sun hakikance cewa Peter Obi ba zai ba ‘yan Nijeriya kunya ba, don haka sun ajiye ƙabilanci a gefe don su zaɓi shugabannin da su ka dace.