Home Labarai Gwamnatin Nijeriya Zata Gina Tashar Wutar Lantarki A Jihar Imo

Gwamnatin Nijeriya Zata Gina Tashar Wutar Lantarki A Jihar Imo

44
0

Gwamnatin tarayya, ta amince da gina tashar wutar lantarki mai karfin megawatt goma a kogunan Otamiri da Nworie da ke birnin Owerri na jihar Imo.

Wannan ya na kunshe ne a cikin wani sako da gwamnatin jihar Imo ta wallafa a shafinta na Twitter, inda ta ce za a gina tashar ne domin sama wa al’ummar Owerri da kewaye isasshiyar wutar lantarki.

Ko da ya ke gwamnatin ba ta ambaci ko naira nawa aikin zai lakume ba, amma wasu manazarta sun bayyana shakku game da yiwuwar aikin.

Sahararren marubuci Dakta Amanze Obi, ya ce ya na ganin yunkurin abin a yaba ne, amma ya na fata dai ba siyasa su ke yi ba, saboda sai a karshen mulkin Buhari ake neman bijiro da wani muhimmin aiki a kudu maso gabas, don haka ya na mamakin yadda za a kammala aikin daga yanzu zuwa lokacin da shugaba Buhari zai bar mulki.