Home Labaru Ɗan Takarar Gwamnan Da Aka Zarga Da Sayen Ƙuri’u Ya Maka Malami,...

Ɗan Takarar Gwamnan Da Aka Zarga Da Sayen Ƙuri’u Ya Maka Malami, Sufeto Janar Kotu

13
0

Ɗan takarar gwamnan Jihar Ogun na jam’iyyar PDP Ladi
Adebutu, ya maka Ministan Shari’a Abubakar Malami da
shugaban ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba da
jam’iyyar APC kotu, bayan fitar labarin abin da binciken ‘yan
sanda ya ƙunsa dangane da zargin shi da sayen ƙuri’u na
Naira biliyan biyu a ranar zaɓe.

Haka kuma, Ladi Adebutu ya maka Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya SSS Yusuf Bichi da Shugaban hukumar EFCC Abdulrashid Bawa da Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Ogun Yemi Sanusi bisa zargin sayen ƙuri’u da aka yi ma shi.

A ƙarar da Adebutu ya shigar, ya bayyana wa kotu cewa tun farko APC ta kai ƙorafi ga Ministan Shari’a Abubakar Malami da EFCC, kuma daga nan ne ‘yan sanda su ka gayyace shi, amma da niyyar idan ya je su kama shi, don kawai su hana shi ko su karkatar da shi daga ƙarar Gwamna Dapo Abiodun a Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Adebutu ya shaida wa kotu cewa, ya na roƙon ta hana Ministan shari’a shugaban ‘yan Sanda hukumomin EFCC da SSS kama shi.

Ya ce su na son kama shi ne kawai don su hana shi shari’ar ƙarar da ya shigar a kan Gwamna Abiodun na jam’iyyar APC, wanda ya yi nasara kan sa da ratar ƙuri’u dubu 14 kaɗai.