Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta nuna damuwar ta a kan zargin da hukumar EFCC ta yi cewa Gwamnan jihar Bello Mohammed Matawalle ya karkatar da kimanin Naira biliyan 70 a lokacin mulkin sa.
APC ta ce, zargin ya biyo bayan kiran da Matawalle ya yi wa hukumar EFCC cewa ta binciki wasu mutane a Fadar Shugaban Ƙasa da wasu daga cikin ministocin Buhari.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar APC a jihar Zamfara Yusuf Idris ya bayyana haka, yayin da ya ke maida martani a kan rahoton hukumar EFCC na karkatar da Naira biliyan 70 da gwamnatin Mohammed Matawalle ta yi.
Jam’iyyar APC, ta bayyana zargin hukumar EFCC a matsayin cin mutuncin Gwamna Matawalle, ta na mai cewa zargin ba ya da tushe balle makama.
Ta ce ya kamata hukumar EFCC ta fara da binciken yawan adadin kuɗin da Jihar Zamfara ta samu a cikin shekaru huɗu da suka gabata, da albashin ma’aikatan ta da ayyukan ci-gaban da aka samar ciki har da ƙoƙarin Matawalle na magance matsalar tsaro da fannin kiwon lafiya da samar da ayyukan yi da hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa.
You must log in to post a comment.