Kamfanin man fetur na kasa NNPC, ya sanar da komawa aikin neman mai a yankin Tafkin Chadi da ke jihar Borno.
NNPC ya dakatar da aikin ne a watan Yuli na shekara ta 2017, bayan wasu mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kai wa ma’aikatan hari har su ka yi garkuwa da wasu.
Bayan yanayin tsaro ya inganta a shekara ta 2022 ne, kamfanin NNPC ya yanke shawarar sake komawa aikin a rijiyar Mai ta Wadi.
Daraktan zartarwa na bangaren aikin neman man Mukhtar Zanna, ya ce su na da kwarin gwiwa a kan aikin saboda su na da bayanai da kuma sabuwar fasaha ta zamani. Kamfanin NNPC, ya ce ya na da kyakkyawan zaton cewa za a samu mai da gas mai yawan gaske a wannan wuri
You must log in to post a comment.