Home Labaru ‘Ƴan Sanda Sun Tarwatsa Ƴan Fashin Daji A Zamfara

‘Ƴan Sanda Sun Tarwatsa Ƴan Fashin Daji A Zamfara

1
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara, ta ce jami’an ta sun
tarwatsa wani yunƙurin ‘yan bindiga na kai hari a wani ƙauye
da ke ƙaramar hukumar Tsafe.

Haka kuma, jami’an ‘yan sandan sun samu nasarar hallaka wasu ‘yan bindigan biyu.

A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Zamfara Mohammed Shehu ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda aka yi artabu tsakanin jami’an ‘yan sandan da ‘yan bindiga.

Sanarwar ta ce baya ga waɗanda aka kashe, wasu maharan kuma sun tsira da munanan raunuka.