Home Labaru  ‘Ƴan Sanda Sun Ceto Mutum 11 Da Aka Sace Kan Hanyar Kaduna...

 ‘Ƴan Sanda Sun Ceto Mutum 11 Da Aka Sace Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja.

179
0

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta ceto mutum 11 daga cikin matafiyan da ƴan bindiga suka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.

Kwamishinan ƴan sandan Kaduna ya ce jami’an su da sojoji sun fatattakki ƴan bindigar inda suka yi nasarar kuɓutar da mutum 11.

A ranar Lahadi ne ƴan bindiga suka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka yi garkuwa da matafiya da dama tareda kashe wani tsohon dan takaran Gwamna a jihar zamfara Alhaji Sagir Hamidu.

Ya Zuwa yanzu dai hukumomi ba su bayyana adadin mutanen da aka kashe da wadanda aka sace ba.

Tuni dai Lamarin ya jefa jama’a musamman direbobi da fasinjoji dake bin hanyar Abuja zuwa Kaduna cikin zullumi.

Hanyar Abuja zu