Home Labaru Ilimi  Hukumar WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2021

 Hukumar WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2021

139
0

Hukumar Shirya Jarabawa ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandire ta shekarar 2021.

Shugaban hukumar a Najeriya, Patrick Areghan ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin anan Abuja.

Yace Jimlar dalibai 1,573,849 ne suka yi rajistar jarabawar a cibiyoyi 19,425 da hukumar ta amince da su a fadin kasar nan.

To sai dai yace 1,560,261 suka zana jarabawar a bana.

Sanarwar ta ce akalla dalibai 1,274,784 ne suka sami nasara a darusa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

Yayinda hukumar ta rike sakamakon jarabawar dalibai kimanin 170,146 da ta kama da laifukan satar jarabawa.

Har ila yau, sanarwar ta ce tuni hukumar ta fitar da sakamakon dalibai 1,256,990, kwatankwacin kaso 80 cikin 100 na daliban da suka zana jarabawar a Najeriya.

Patrick ya kara da cewa suna nan suna kokarin fitar da sakamakon ragowar daliban, wadanda ya ce wasu matsalolin da suka samu da wasu daga cikin darusan ne suka haifar musu da tsaikon.

Daga karshe Hukumar ta umurci dalibai suyi amfani da lambobin sirrin dake jikin katin da suka yi amfani das hi domin wajen Rubuta jarabawar domin duba sakamakon su.

Leave a Reply