Home Labaru Ƙungiyar Ohanaeze Ta Buƙaci Gwamnati Ta Kai Nnamdi Kanu Kotu

Ƙungiyar Ohanaeze Ta Buƙaci Gwamnati Ta Kai Nnamdi Kanu Kotu

17
0

Gabanin gurfanar da shugaban ‘yan A-Waren Biafra Nnamdi Kanu a gaban kotu ranar Alhamis, ƙungiyar ƙabilar Ibo ta Ohanaeze ta bukaci gwamnatin tarayya ta tabbatar an kai shi kotu.

Kungiyar, ta ce bayyanar Kanu a kotu YA na da muhimmanci, don a nuna wa duniya cewa Nnamdi Kanu ya na ciki ƙoshin lafiya kuma za a yi ma shi adalci a lokacin shari’a.

Idan dai ba a manta ba, ƙungiyar IPOB ta yi barzanar rufe duk ayyuka a yankin Kudu maso gabashin Nijeriya idan ba a kai Nnamdi Kanu Kotu ba.