Shugaban Ƙasar Ghana mai barin gado Nana Akufo-Addo na shan suka a shafukan zumunta bayan ya ƙaddamar da mutum-mutuminsa da kan sa a yankin Yammacin ƙasar.
A cewar ministan yankin Kwabena Okyere Darko-Mensah, an ƙirƙiri makwafin ne domin girmama ayyukan da shugaban ya yi lokacin da yake kan mulki,
Sai dai ‘yan Ghana da dama na ta tsokanar mutum-mutumin, wanda aka girke a wajen wani asibiti da ke birnin Sekondi, suna cewa yabon kai ne.
A cewar wani ɗan majalisar adawa Emmanuel Armah Kofi-Bash cikin wani saƙon X Mazauna yankin Yamma sun fi ƙarfin wannan yabon kan.
Nana Akufo-Addo wanda zai sauka daga mulki a watan Janairu bayan wa’adi biyu, ya yi kurin cewa ya cika kashi 80 cikin 100 na alƙawurran da ya ɗaukar wa ‘yan Ghana.