Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kuɗin shekara ta 2025 a gaban majalisar dokokin jihar.
Kasafin kuɗin na bana wanda shi ne na biyu da gwamnan ya gabatar ya kai fiye da naira biliyan 500.
Duk da kasancewar jihar cibiyar harkokin kasuwanci amma ta na sahun gaba wajen yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, abin da ya sa gwamnati ta ware fiye da kashi 31 na kasafin ga bangaren ilimi.
Bangarorin da aka ware wa kudin sun kunshi Ilimi: Naira biliyan 168.4 (kashi 31%), sai Lafiya: Naira biliyan 90. 6, sai Sufuri: Naira biliyan 12. 2, sai Harkokin noma: Naira biliyan 21.03,
sai Albarkatun ruwa: Naira biliyan 27. 23, da kuma Samar da ababen more rayuwa: Naira biliyan 70.78.














































