Jacob Zuma, zai ƙaddamar da manufofin sabuwar jam’iyyar sa ƙasa da mako biyu kafin babban zaɓen kasar.
Komawar sa fagen siyasar, ta hanyar jam’iyyar sa ta, na barazanar hana jam’iyya ANC samun rinjayen da take buƙata.
Jam’iyyar sa ta ɗauki sunan wani ɓangare na jami’yyar ANC mai ɗauke da makamai da aka wargaza a baya.
ANC dai ta nemi ta yaƙe shi a kotu amma ba ta yi nasara ba.
To sai dai har yanzu tsohon shugaban na fuskantar ƙalubale, bayan da hukumar zaɓen ƙasa ta shigar da ƙara a kan sa














































