Home Home Zulum Ya Raba Buhunnan Shinkafa Don Rage Matsin Rayuwa

Zulum Ya Raba Buhunnan Shinkafa Don Rage Matsin Rayuwa

37
0

Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya sa ido a kan shirin rage raɗaɗi da ya ƙunshi tallafin abinci ga iyalai dubu 2  a mazaɓar Mafoni da ke birnin Maiduguri.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Mallam Isa Gusau ya fitar, ta ce manufar rabon abincin ita ce rage raɗaɗin cire tallafin man fetur, kuma yayin rabon, an ba kowane gida buhun shinkafa da wake.

Gwamna Zulum, ya ce an zaɓo waɗanda su ka ci gajiyar shirin ne daga mazaɓu 27 a faɗin Maiduguri, da kuma mazaɓu 12 daga ƙaramar hukumar Jere.

Sanarwar ta ce rabon abincin, wanda ya ƙunshi buhunnan shinkafa dubu 54, da buhunnan wake 54,000, an bada su ne ga magidantan da su ka fi buƙata a ƙananan hukumomin jihar biyu.

Ta ce gwamnatin Zulum ta tashi haiƙan wajen neman dabarun da za su rage illar da hauhawar farashin man fetur ta haifar a kan talakawa, ta hanyar tabbatar da ganin abinci da sauran muhimman abubuwa ga masu tsananin buƙata.

Leave a Reply