Home Home Muhawara Kan Keyamo Ta Janyo Dakatar Da Zaman Majalisar Dattijan Najeriya

Muhawara Kan Keyamo Ta Janyo Dakatar Da Zaman Majalisar Dattijan Najeriya

47
0

Majalisar Dattawa ta dakatar da ci-gaba da aikin tantance ministocin da ake sa ran ta kammala a ranar Ltinin din nan, bayan muhawara ta yi zafi tsakanin ‘yan majalisar lokacin da ake tantance lauya Festus Keyamo.

Muhawarar dai ta barke ne, lokacin da wani Sanata ya janyo hankalin majalisar a kan abin da ya kira cin fuskar da Festus Keyamo ya yi wa majalisa, lokacin da ya ke rike da mukamin minista a gwamnatin Buhari.

Dan majalisar ya ce a wancan lokacin, Keyamo ya yi biris da shawarar da majalisa ta gabatar da kuma kin amsa gayyatar ta domin amsa tambayoyi dangane da Shirin.

Wannan ya sa dan majalisar ya bukaci Keyamo ya yi bayani a kan dalilin da ya say a raina majalisa a wancan lokacin, inda nan take mahawara ta kaure, lamarin da ya sa shugaban majalisar Godswill Akpabio ya dage zaman majalisar tare da garzayawa zuwa fadar shugaban kasa bisa rakiyar mukarraban sa domin ganawa da shugaba Tinubu.

Leave a Reply