Home Labaru Operation Lafiya Dole Ta Gano Ramuka ‘Yan Boko Haram A Borno

Operation Lafiya Dole Ta Gano Ramuka ‘Yan Boko Haram A Borno

375
0
Operation Lafiya Dole Ta Gano Ramuka ‘Yan Boko Haram A Borno

Hedkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar Operation Lafiya Dole ta gano cewa mayakan Boko Haram da ke yankin Isari a karamar hukumar Gamboru Ngala sun haka wasu ramuka a matsayin tarko.

Rundunar ta tabbatar da cewa, ta gano ramuka da aka haka ne a kauyukan Gulwa da Diime da Musiri da Wuri Bari da Mada da Sangaya da Jarawa da Mutu da Isari da Mudu.

A cikin wata takarda da rundunar ta fitar, ta ce wasu daga cikin manyan mayakan Boko Haram sun mika kan su ga rundunar sojin Nijeriya.

Shugaban sashin yada labarai na rundunar Manjo Janar Enenche  ya ce, a lokacin da rundunar sojin Nijeriya ke gab da samun nasarar gamawa da mayakan Boko Haram, wasu daga cikin ‘yan ta’addan na mika wuya bayan tarwatsa maboyar su.

Dakarun soji da ke sansani na 11 a garin Gamboru, sun gano wata maboyar ‘yan ta’addan, inda suka haka ramuka, sannan sun kama ‘yan ta’adda uku tare da kwace bindiga kirar AK 47 guda daya a hannun su.