Home Home ZULUM Ya Ƙaddamar Da Motoci 80 Don Jigilar Manoma Zuwa Gona A...

ZULUM Ya Ƙaddamar Da Motoci 80 Don Jigilar Manoma Zuwa Gona A Borno

128
0

A wanu yunkuri na rage wa talakawan sa raɗaɗin cire tallafin man fetur, Gwamna Zulum na Jihar Borno ya samar da manyan motoci kirar Bas guda 80 da na ɗaukar kaya domin jigilar manona zuwa gonakin su kyauta.

A ranar Talatar da ta gabata ne, gwamna Zulum ya saki motocin domin fara aiki kamar yadda aka tsara.

Wannan dai ya na zuwa ne, ƙasa da mako guda bayan mayaƙan Boko Haram sun kai hare-hare a yankunan Wulari da Bulajimban, inda su ka kashe manoma takwas tare da yi wa manoma bakwai yankan rago.

Yayin da ya ke duba lafiyar hanyar da manoman za su yi amfani da ita, Gwamna Zulum ya samu tattaunawa da sojoji a kan yadda za a riƙa jigilar manoman cikin nasara.

Akarshe ya yi kira ga jami’an tsaro su ƙyale manoma su riƙa zuwa gonakin su, saboda a cewar sa, matsalar ƙarancin abinci ta fi tsanani a kan ta tsaro.

Leave a Reply